Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani, Bayan Fara Rijistar DE
An fara rijistar tsarin shiga Jami’a kaitsaye (DE), a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairun da ya gabata, ya yin da aka tsara rufe rijistar, a ranar 28 ga watan da mu ke ciki na Maris.
Ana sayar da Form ɗin DE ne, akan farashin Naira 6,700, za kuma a iya rijistar ne kawai a JAMB State Offices (Ofisoshin JAMB na Jihohi).
Wajibi ne kuma ga wanda zai cike DE ɗin ya kasance yana da shaidar kammala karatun Diploma ta ƙasa (ND), Babbar Diploma ta ƙasa (HND), IJMB, ko Digirin Jami’a.
Bugu da ƙari wajibi ne, ga dukkannin wanda ke son cike DE ɗin ya mallaki aƙalla Credits 5, da su ka haɗarda Lissafi da Turanci (English & Mathematics) a sakamakonsa na kammala makarantar Sakandire (O’Level), a zaman da bai wuce guda biyu ba (In Not Morethan 2 Sittings).
A Yayin Rijista Kuma, Wajibi Ne Ɗalibi Ya Gabatar Da Waɗannan Abubuwan :
a) Registration/Matriculation Number ɗinsa ta makarantar da ya kammala.
b) Qualification ɗin da ya samo.
c) Matsayin Makarantar.
Wasu Ƙarin Sharuɗɗan Ga Ɗaliban DE:
a) Ɗaliban da su ka cika DE da Awaiting Result, sakamakon jiran sakamakonsu na A’Level ɗin UMS/UPER/NABTEB da su ke yi, wajibi ne su yi Uploading ɗin Admission Letters da Registration Templates ɗinsu, a ya yin rijista.
b) Duk ɗalibin da ba awaiting Result ya ke ba, wajibi ne, ya yi Uploading ɗin A’Level Result, O’Level Result, da DE Registration Template ɗinsa, a ya yin rijista.
c) Ba za a bawa Ɗalibi Admission ba, har sai an aikewa makarantar da ya kammala sakamakonsa, ta tantance, sannan ta sake yi wa JAMB uploading ɗinsa a ‘CAPS MAIL’ (Result/Certificate Verification).
d) Duk ɗalibin da ya ke da kwalin Cambridge, wanda ya ke ƙasa da shekarar 2018 zai halarci Cambridge ɗin ne kaitsaye, domin yi masa Verification. Kuma verification ɗin zai iya ɗaukar kwanaki 28 (kamar yadda makarantar ta bayyana) daga nan kuma za a aikewa da JAMB sakamakon, sai ya yi reflecting a e-Facility prohle na Ɗalibin.
e) Za a iya karɓar Statement Result (a madadin Certificate) domin yin rijista, idan ya kasance ba a haura shekaru 3 da kammala karatu ba.
KU SANI: Akwai damar converting daga JAMB UTME zuwa DE, idan ya kasance ba a saki sakamakon A’Level ɗin Result ɗin ɗalibi ba a lokacin rijista, kuma ya bayyana hakan tun a wurin rijista.
Domin neman ƙarin bayani : 08039411956.
Rubutawa: Miftahu Ahmad Panda
08039411956