ZamantakewaRahotanni

Abubuwan Da Yakamata Ku Sani Game Da Ranar Hausa Ta Duniya

A Yau ne, ake bikin Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake tunawa da ita a duk ranar 26 ga watan Agusta.

 

Ƙiyasi na baya-baya da aka yi cikin shekarun da suka wuce, a cewar Farfesa Muhammad Bunza, ya nuna Hausawa sun kai miliyan 150. Amma dai masana na ganin cewa haƙiƙanin yawan Hausa ya yi matuƙar zarce haka.

 

Ranar Hausa (Ko kuma #RanarHausa) da turanci Hausa Day, Rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta. an fara bikin farko a shafukan sada zumunta musamman ta shafin twitter da niyyar hada L1 da L2 na masu magana da harshen Hausa. An zaɓi ranar 26 ga watan Augusta domin tuna ranar da aka ƙirƙiro haruffan “ƙ” da “ɗ” da “ɓ” wanda babu su a haruffan Turanci.

 

A Yayin bikin na cika shekara 6, mutane fiye da 400,000 suka gudanar da bikin ta yanar gizo da wasu kasashen da Hausawa suke zaune a sassa daban daban na duniya irinsu Faransa, Amurka, Kamaru, Ghana, Nijar, da Najeriya, kuma a irin wanan rana hausawa na duniya na cika shafukan zumunta da da zantuttuka masu nuna Alfahari da yarensu, wasu wajajen sukan shirya bukukuwa a wanan rana.

 

A kowace shekara idan ranar ta zagayo ma’abota shafukan sada zumunta na yin amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara. Daga bisani kuma a shekarar 2018 aka fara gudanar da bukuwa na zahiri a gidan ɗan Hausa da wasu ƙasashe a fadin duniya kamar Ghana.

 

Asali

 

Ranar Hausa dai ta samo asali ne a shekarar 2015 bayan ɗan jarida Abdulbaqi Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta suka ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da harshen Hausa za su haɗu su tattauna ci gaba da kalubalen da harshen ke fuskanta a karni na 21. Kuma ana bikin Ranar Hausar ne a 26 ga watan Agustan kowace shekara a Duniya.

 

Muhimmanci

 

An ƙirƙiri wannan rana ce domin duba da mahinmancin ta ko kuma mahinmancin da zata bada. Makasudin wannan rana dai itace. Domin ciyar da yaren hausa gaba, al’ummar su, al’adunsu da kuma samun hadin kan hausawa a duniya baki daya.

 

A kowace shekara idan ranar ta zagayo ma’abota shafukan sada zumunta ke yin amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara.

 

Nasarorin da aka samu

 

Wadanda suka ƙirƙiro wannan ranar sun ce sun yi haka ne domin tuna wa da al’ummar Hausa game da muhimmancin harshen da yadda za a ciyar da shi gaba.

 

Sannan kuma ranar ta kasance a matsayin wata rana da ake ƙalubalantar al’ummar Hausawa domin fiddo da sabbin bincike da nazarce-nazarce domin habbaka harshen na Hausa.

 

Ana fatan harshen Hausa zai samu karɓuwa nan ba da jimawa ba cikin harsunan amfani na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar haɗa kan ƙasashen Afirka ta AU da ma Kungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS.

 

✍️Saliadeen Sicey.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button