Abubuwan Tunawa Ga Talaka, A Tsohuwar Gwamnatin Ƴar Adu’a
A yau (Lahadi) 5 ga watan Mayun 2024 ne, tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Umaru Musa Ƴar Adu’a, ya ke cika shekaru 14 da rasuwa.
Ƴar Adu’a, ya rasu ne, a ranar 5 ga watan Mayun 2010, ya na da shekaru 59 a duniya.
Ya kuma rasa ransa ne, bayan fama da rashin lafiya, inda bayan rasuwarsa Mataimakinsa, Good luck Ebele Jonathan, ya ɗare kan kujerar shugabancin ƙasar.
Abubuwan da Talakawa ba za su iya mantawa da su, a zamanin shugabancin Ƴar Adu’a ɗin ba dai, su ne arahar kayayyaki da aka samu, wanda hakan ya sanya aka rayu cikin walwala, kafin faɗawa halin ƙaƙanikayin da ake ciki a yanzu.
Ga farashin wasu daga cikin kayayyakin amfani, a lokacin Shugabancin Ƴar Adu’a ɗin:
• Litar Fetur – Naira 65.
• Litar Diesel – Naira 112.
• Litar Kalanzir – Naira 50.
• Buhun Shinkafa – Naira 3,500.
• Buhun Sugar – Naira 7,000.
• Buhun Siminti – Naira 750.
• Buhun Taki – Naira 2,500.
• Kuɗin Aikin Hajji – Naira 600,000.
• Kujerar Umrah – Naira 250,000.