Kiwon Lafiya

Adadin Mutanen Da Ke Fama Da Mummunar Ƙiba Na Barazanar Kaiwa Biliyan 1.53 A Faɗin Duniya

Wani rahoto da sashen bibiyar masu fama da ƙiba na duniya ya fitar, ya bayyana yadda adadin masu ƙiba daga ɓangaren Yara masu ƙananun shekaru, da Manyan da ke faɗin duniya ke cigaba da ƙaruwa, wanda hakan ke fito da buƙatar ɗaukar matakan da su ka dace, wajen taƙaita faɗaɗuwar lamarin.

Yawaitar masu fama da ƙibar kuma, na sake fito da irin tazarar da ke akwai a tsakanin fannin kiwon lafiya da cimakar al’umma, duba da yadda yaɗuwarta ke cigaba da kasancewa wutar daji.

Wata ƙididdiga da sashen kula da masu ƙibar ya samu tozali da ita, ta bayyana cewar kaso 79 na mutanen duniya da su ka mallaki hankalin kansu suna da nauyin da ya zarce wanda ake buƙatar a samu jikkunansu, za kuma a samu ƙaruwar wannan adadi zuwa kaso 88 cikin 100 zuwa shekarar 2035.

Ana kuma gabatar da bikin ranar masu ƙiba/teɓa ta duniya a dukkannin ranar 4 ga watan Maris ɗin kowacce shekara.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button