Adam Zango Ya Saki Sabon Kundin Waƙoƙinsa
Fitaccen Mawaƙi, kuma Jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango, ya saki sabon kundin waƙoƙinsa (Album), mai suna ‘Babu Lokaci’.
Zango, ya bayyana sakin sabon kundin waƙoƙin nasa ne, ranar Litinin ta shafukansa na kafafen sada zumunta, bayan da ya wallafa hoton bangon kundin (Cover Photo).
Kundin kuma na ɗauke da waƙoƙi 15 ne, da su ka haɗarda: Diana, Manyan Mata, Kulle, Amataha, Ba Faɗa Bane, Soyayya Daɗi, Allazy Waheedy, Suna Linzami, da Na Baki Soyayya.
Sauran waƙoƙin da ke cikin kundin su ne: Ya Kasuwa, Allah Gyara, Ƴar Mama, Amarya, Wane Yaro, da Rashin Tawakkali.
Kundin kuma, ya kasance kundi na farko da Jarumin ya saki, bayan shigowar sabuwar shekarar 2024.
Za ku iya samun kundin akan: https://fanlink.to/uv5q0