AFCON: Najeriya Ta Samu Nasarar Zuwa Wasan Ƙarshe
Tawagar Najeriya ta Super Eagles, ta samu nasarar zuwa wasan ƙarshe a gasar Kofin Ƙasashen Afirka, bayan da ta lallasa tawagar ƙasar Afirka Ta Kudu ta Bafana-Bafana a bugun daga kai sai mai tsaron raga da suka fafata.
An tashi wasa mintuna 90 ne dai, tawagar Najeriya na da ƙwallo 1 ya yin da ita ma Afirka ta Kudu ke da tata ƙwallon guda 1.
Bayan ƙarin mintuna 30 ɗin da aka je ma dai, bata sauya zani ba, ƙasashen sun ci gaba da kasancewa kunnen doki, wanda hakan ya tilasta zuwansu bugun daga kai sai mai tsaron raga (Penalty).
A bugun fenareti ɗin ne kuma, Najeriyar ta lallasa Bafana Bafana da ci 4 da 2.
A yanzu dai, Najeriyar za ta fafata wasan ƙarshe ne, tsakaninta da dukkannin wacce ta samu nasara a tsakanin ƙasashen Demokraɗiyyar Congo da Ivory Coast, a wasan da za su fafata da misalin ƙarfe 9 na daren yau.
Ita kuwa, Afirka ta Kudun za ta fafata wasan neman na uku ne, a ranar Asabar.