AFCON: Najeriya Ta Samu Nasarar Zuwa Semi Final, Bayan Lallasa Angola
Tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles, ta samu nasarar zuwa wasan Semi Final, a gasar kofin ƙwallon ƙafar ƙasashen Afirka, da ke cigaba da gudana ƙasar Ivory Coast.
Najeriya dai, ta samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen na ƴan huɗu ne, bayan da ta lallasa tawagar ƙwallon ƙafar Angola da ci 1 da nema, a wasan da su ka fafata da yammacin yau (Juma’a), 2 ga watan Fabrairun 2024.
Najeriyar kuma, za ta fafata wasanta na gaba, cikin tawagar ta ƴan huɗu ne, tsakaninta da wacce ta samu nasara cikin ƙasashen, Cape Verde da Afirka ta Kudu, a wasan da za su fafata, a gobe (Asabar) 3 ga watan Fabrairun 2024.
Tawagar ta Najeriya dai, na cigaba da nuna matuƙar ƙwazo a gasar, bayan da ta lashe dukkannin wasannin da ta fafata, idan aka cire wasanta na farko, da ta yi cancaras.