Wasanni
AFCON: Yadda Najeriya Ta Kori Kamaru, Tare Da Tsallakawa Zagayen Ƴan 8
Tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles, ta lallasa ƙasar Kamaru, da ci 2 da nema, a wasan da su ka fafata a daren jiya (Asabar), a cigaba da buga wasannin ‘sili ɗaya kwale’ na zagayeb ƴan 16 a gasar cin Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON), da ƙasar Ivory Coast ke karɓar baƙunci.
Hakan kuma, ya bawa tawagar ta Super Eagles, damar tsallakawa zagayen ƴan 8 (Quarter Final), tare da cire ƙasar ta Kamaru daga gasar AFCON ɗin ta bana.
A yanzu Najeriya kuma, za ta buga wasanta na gaba ne, da ƙasar Angola, a ranar 2 ga watan gobe na Fabrairu, domin tantance zakarar da za ta tsallaka matakin ƴan 4, daga cikinsu.