Wasanni
Ahmed Musa Ya Kai Ziyara Fadar Gwamnatin Kano
Jagoran ƴan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (Super Eagles), Ahmed Musa, ya kai ziyara fadar gwamnatin jihar Kano, a ranar Talata.
Ahmed Musa, ya ce ya kai ziyarar ne domin miƙa godiya ga gwamna, Abba Kabir Yusuf, kan irin goyon baya da ƙwarin guiwar da gwamnatin Kanon ta bashi, tare da sauran ɗumbin al’ummar jihar, ya yin da ake taka leda a gasar Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) na shekarar 2024, da aka gudanar a ƙasar Cote D’Ivoire.
Ahmed Musa, ya kuma sha alwashin tallafawa harkokin wasanni a jihar ta Kano, da iya ƙarfin da Allah ya hore masa.
A nasa jawabin, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yabawa yunƙurin ɗan wasan, tare da yi masa bangajiya.