Labarai
Aisha Bura Ta Lashe Zaɓen Shugabancin Ƙungiyar Ƴan Jaridu Mata Ta Ƙasa
An zaɓi, Aisha Ibrahim Bura, wacce ke wakiltar jihar Borno a ƙungiyar Ƴan Jaridu Mata ta ƙasa (NAWOJ), a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar ta ƙasa baki ɗaya.
Bura, ta samu wannan nasara ne, a ya yin zaɓen da wakilan ƙungiyar na ƙasa su ka gudanar, a daren Asabar, bayan da ta doke abokiyar takararta, Ladi Bala.
A ya yin zaɓen na Asabar kuma, an kaɗawa Wasilan Ladan ƙuri’a a matsayin Sakatariyar ƙungiyar ta ƙasa, Lillian Okonkwo matsayin Mataimakiyar shugaba ta ƙasa, Sai Jamila Abubakar Chinwe da ke matsayin Auditor Janar.
Tuni kuma aka rantsar da sababbin shuwagabannin ƙungiyar ta NAWOJ, a Cibiyar Mata ta Dr. Maryam Babangida, da ke babban birnin tarayya Abuja, wanda anan ne aka gudanar da zaɓen.