Akwai Yiwuwar Ƙungiyar Ƙwadago Ta Nemi Naira 794,000 Ko 447,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Akwai hasashe mai ƙarfi na yiwuwar ƙungiyar ƙwadago ta nemi Naira Dubu 794,000 ko 540,000 ko kuma 447,000, a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar nan, hakan kuma ya zo ne bayan taron jin ra’ayi da ƙungiyar ta gudanar, ranar Alhamis (Yau) a rassanta na shiyya-shiyya (Zonal), da ke Lagos, Kano, Enugu, Akwa Ibom, Adamawa, da Babban Birnin Tarayya Abuja.
A ya yin taron na yau kuma, NLC reshen Kudu Maso Yamma, ta buƙaci a nemi Naira 794,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin, ya yin da reshen Kudu Maso Gabas kuwa suka amince da Naira 540,000 da 447,000.
A yanzu kuma, ƙungiyar za ta ƙididdige adadin kuɗin da za ta buƙata ne, bayan gudanar da taron zartarwarta na ƙasa.
Idan mai bibiyar Rariya Online zai iya tunawa dai, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero, ya taɓa bayyana yiwuwar ƙungiyar ta nemi Naira 500,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, a ranar 11 ga watan Fabrairun da ya gabata, ya yin tattaunawarsa da tashar Talabijin ta Arise, inda ya ce muddin aka ci gaba da samun hauhawar farashi, to ba abin mamaki bane ma ƙungiyar ta nemi Naira miliyan guda a matsayin mafi ƙarancin albashi, ga ma’aikatan ƙasar nan.
Taron jin ra’ayin da aka gudanar, a shiyyoyin ƙungiyar guda shida, a yau kuma, ya samu sanya bakin ƴan ƙungiyar ƙwadago, gwamnonin jihohi, ministoci, ƙungiyoyin ma’aikata, har ma da ma’aikatan masana’antu masu zaman kansu, dan ganin mafi ƙarancin albashin da za a amince da shi ɗin, ya yi dai-dai da halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi.