Kiwon Lafiya

Akwai Yiwuwar Ɓarkewar Cholera Da Typhoid Ga Mutanen Da Ke Amfani Da Ƙanƙara

Masana lafiya sun yi gargaɗi kan yiwuwar ɓarkewar ciwon Typhoid da Cholera ga al’ummar Najeriya, sakamakon dawowa amfani da ƙanƙara gadan-gadan da su ka yi, biyo bayan sirkawar yanayin zafi.

Najeriya dai, guda ce cikin jerin ƙasashen da ciwukan na Cholera da Typhoid su ka samu gindin zama, sakamakon amfani da gurɓataccen ruwa da mafi yawan al’ummar ƙasar ke yi.

Bayan sirkawar zafi a baya-bayan nan kuma, jama’a da dama sun shiga amfani da ƙanƙara ba dare ba rana, sakamakon rashin wadataccen kuɗin mallakar Ruwan Leda, wanda a wasu sassan farashinsa ke kaiwa Naira 50.

Sai dai, inda gizo ke saƙar shi ne, yadda da dama daga cikin masu sarrafa ƙanƙarar ke amfani da gurɓataccen ruwa wajen samar da ita, wanda kuma hakan ke haifar da gagarumar illa ga lafiyar waɗanda su ka yi amfani da ita.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button