Akwai Yiwuwar Emefiele Zai Gudanar Da Bikin Kirsimeti A Gidan Gyaran Hali
Alamu na nuni da cewar, tsohon Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, Godwin Emefiele, zai yi bikinsa na Kirsimeti a gidan ajiya da gyaran hali na Kuje, bayan da babbar kotun tarayya da me Abuja, ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar da aka maka shi, bisa zarginsa da yin amfani da madafar iko, wajen aikata badaƙala, ya yin da ludayinsa ya ke kan damu.
Daga cikin zarge-zargen da ake masa dai, akwai bayar da kwangilar shigo da wasu Motoci kimanin 43 waɗanda kimarsu ta kai kimanin Naira biliyan 1.2 ba bisa ƙa’ida ba, daga shekarar 2018 zuwa 2020.
Bayan gurfanar da shi a gaban Kotun ne kuma, sai Kotun ta umarci a tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje, kafin buƙatar bayar da shi beli da aka shigar a gaban Kotun, tun a ranar 22 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, kuma tuni Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Muazu ta bada belin Emefielen kan zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 300.
Kuma Alƙalin ya ce wajibi ne Emefiele ya gabatar da masu tsaya masa guda biyu waɗanda su ke da takardun shaidar zama, tare da mallakar kadarori a Maitama.
Ana kuma tsammanin Emefiele zai yi bikin kirsimeti a gidan gyaran halin ne, saboda gaza cika sharuɗɗan belin da ya yi, har zuwa zaman da aka gudanar, inda aka hangi Jami’an gidan ajiya da gyaran halin sun sake tasa ƙeyasarsa.
An kuma ɗage cigaba da sauraron shari’ar ne, zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2024.