Akwai Yiwuwar Farashin Ruwan Leda Zai Kai Naira 100, Duk Guda 1
Ƙungiyar masu samar da ruwan leda, da aka fi sani da Pure Water (ATWAP), ta koka kan yadda farashin kayayyakin da ake aiki dasu wajen killace ruwan ke cigaba da ƙaruwa, tare da ƙaruwar kuɗaɗen harajin da ake karɓa.
Ƙungiyar ta kuma yi gargaɗin cewar, hakan zai iya sanyawa farashin Ruwan Ledar ya yi tashin gwauron zabi, a ƙasar nan.
Shugabar ƙungiyar ta ƙasa, Dr. Clementina Ativie, ita ce ta bayyana hakan, a ya yin wani taron Manema Labarai da ATWAP ɗin ta shirya, a birnin Lagos.
Clementina, ta kuma ce akwai yiwuwar za a fara sayar da ‘Pure Water’ ɗin akan Naira 100 kowanne guda, a nan gaba kaɗan.
Ta kuma koka kan yadda aka tsame ƙungiyar daga dukkannin wani nau’i na tallafin Gwamnati, inda a madadin basu tallafinma, sai aka nin-ninka harajin da aka ƙaƙaba musu.