Akwai Yiwuwar Na Nemi Diyyar Miliyan Ɗari Biyar A Kotu, Kan Ƙarar Da Na Kai Rarara – Alhaji Sani
Fitaccen Ɗan Siyasa, Mai fafutukar kare kima, da martabar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya ce akwai yiwuwar ya nemi diyyar Naira 500,000,000.00 a wajen Mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya yin da aka fara sauraron shari’ar da ya gurfanar da shi, a gaban Kotu.
Sani Ahmad, ya bayyana hakan ne, a ranar Asabar, ta shafinsa na kafar Sada Zumunta ta Facebook, Inda ya ce, zai nemi a biya shi diyyar ne, sakamakon ɓata masa rai da Rararan ya yi, sanadiyyar kalamansa, akan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
“Akwai yuwar na nemi diyyar Miliyan dari biyar (N500,000,000.00) a kotu wajen Rarara saboda bata min rai da yayi sanadiyyar kalansa akan Baba Buhari.
“Ina kan nazari”, a cewarsa.
A ranar 1 ga watan Nuwamban da mu ke ciki ne dai, Fitaccen Ɗan Siyasar, ya shigar da Mawaƙin ƙara, a gaban Kotu, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya jawo tunzuri a tsakanin al’ummar ƙasa.
Kuma tuni Kotun ta sanya ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar da za ta fara sauraron shari’ar.
Idan ba a manta ba dai, Mawaƙi Rarara, ya zargi Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne, da damalmala sha’anin ƙasar nan, kafin miƙata ga sabon shugaba, Alhaji Bola Ahmed Tinubu.
Da dama daga cikin al’umma kuma, sun kalli kalaman na Rarara ne, a matsayin butulci ga tsohon shugaban, ya yin da wasu kuwa, ke ganin kalaman nasa sun yi dai-dai, sai dai sun zo ba a gaɓar da ake buƙatarsu ba.