Alƙalin Babbar Kotun Nasarawa Ya Mutu
Sabon Alƙalin Babbar Kotun jihar Nasarawa, Tanze Benjamin Makama, ya mutu.
Makama, ya rasa ransa ne, ranar Talata, 5 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki, bayan fama da gajeriyar jinya.
An kuma naɗa shi, a matsayin Alƙalin Babbar Kotun Nasarawa ne, a ranar 29 ga watan Disamban 2023 da ta gabata.
Da ya ke bayyana alhini kan mutuwarsa, shugaban ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa reshen Keffi, Nuhu J. Egya, ya bayyana mutuwar Alƙalin a matsayin gagarumin rashi.
Inda NBA ɗin ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga Iyalan mamacin, tare da roƙon Allah Subhanahu Wata’ala ya basu haƙurin jure rashinsa.
Ka zalika, ƙungiyar ta ƙara da miƙa saƙon ta’aziyyarta ga Alƙaliyar Alƙalai ta jihar, Mai Shari’a Aisha Bashir Aliyu, tare da dukkannin masu ruwa da tsaki a fannin shari’a kan wannan gagarumin rashi na, Mai Shari’a Tanze Makama.