Alhaji Sani Ya Caccaki Marasa Kishin Arewa
Fitaccen Ɗan Jaridar nan, mamallakin Jaridun yanar gizo na Rariya Online da Karamchi, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya soki marasa kishin yankin Arewacin Najeriya.
Alhaji Sani, ya bayyana sukar tasa ne, a matsayin martani kan kiran da wasu ƙungiyoyin fararen hula sama da 200 su ka yi, ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya karrama Ministocin tsaron ƙasar nan. Inda ya wallafa martanin, a shafinsa na kafar sadarwa ta Facebook, da yammacin ranar Alhamis, ya na mai cewa, wasu ko kifar da yankin na Arewa za a yi su koma kudu, muddin za su samu kuɗi, to basu da matsala.
“Wasu fa ko kifar da arewa za’ayi su koma kudu Indai zasu samu kudi toh basu da matsala da hakan.”, a cewarsa.
Alhaji Sani Zangina dai, na ganin cewar, shuwagabannin tsaron basu cancanci yabo ba, duba da yadda har yanzu, ake cigaba da fuskantar ƙalubalen tsaro, a wasu jihohin Arewacin ƙasar nan, irinsu: Katsina da Sokoto.
Ka zalika, ya shawarci ire-iren waɗannan mutane da su sani, basu da yankin da ya wuce Arewa, kuma Arewacin Najeriya ita ce mutuncinsu.
“Yankinka ne Mutunchin ka ya kamata kasan wannan.”, a cewarsa.
Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya kasance guda daga cikin ɗai-ɗaikun Attajiran da ke fitowa, domin bayyana kishinsu ga yankin Arewacin Najeriya ƙarara, tare da yin amfani da dukkannin wata dama da su ke da ita, wajen ɗaga martaba, da kimar yankin.