Zamantakewa

Alhaji Sani Ya Gwangwaje Matashin Da Ya Yi Tattakin Kai Masa Ziyara Da Kyautar Fuloti

Fitaccen Ɗan Jarida, Ɗan Kasuwa, Kuma Ɗan Siyasa, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya gwangwaje wani matashi mai suna, Nuhu Umar, mazaunin garin Suleja, da kyautar danƙareren Fuloti, wanda kimarsa ta haura Naira 500,000.

Alhaji Sani, ya bawa Matashin wannan gwagwgwaɓar kyauta ne, bayan da ya yi tattaki daga garinsu na Suleja, zuwa jihar Nasarawa, domin kaiwa Fitaccen Ɗan Jaridar ziyara, da nufin bayyana farincikinsa kan ƙarar da Alhajin ya maka Rarara a gaban Kotu, wanda hakan ke bayyana soyayyarsa ƙarara ga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Kafin gudanar da tattakin a yau (Labara) dai, sai da matashin ya sanar da wannan shiri nasa, ta shafin Facebook, tun a yammacin ranar Talata.

Haka zalika, bayan rabauta da kyautar filinma, Matashin ya wallafa hoton da su ka ɗauka, a ya yin da ya kaiwa, Alhaji Sani Ahmad Zangina ɗin ziyara, tare da saƙon godiya bisa gagarumar kyautar fulotin da ya rabauta da ita.

“Alhamdulillah na haduda alhaj sani Sani Ahmad wanda yakai rara kara a kotu
Ya kuma min sha tara ta arziki yabani
Kyautar fili 1plot wanda darajar ta yakai ₦500.000🙏🤲🙏”. a cewar Matashi Nuhu Umar.

Idan ba a manta ba, ko a jiya ma, sai da muka kawo muku Labarin Magidancin da ya yi tattaki har tsawon kwanaki bakwai, domin kaiwa Alhaji Sani Ahmad Zangina ɗin ziyara, tun daga garin Argungu na jihar Kebbi, har zuwa jihar Nasarawa, domin kaiwa Fitaccen Ɗan Jaridar ziyarar ƙafa da ƙafa.

Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya maka Mawaƙin Siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara ne dai a gaban Kotu, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya tunzura al’umma, bayan da ya zargi Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da yin dama-dama da ƙasar nan, kafin miƙata ga shugaban ƙasa na yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button