Zamantakewa

Alhaji Sani Ya Shawarci Masu Buƙatar Ya Maka Iyayen Gidan Rarara A Kotu

Ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook, Alhaji Sani Ahmad Zangina, wanda shi ne Ɗan Jaridar da ya maka Mawaƙin Siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara a gaban Kotu, ya shawarci masu bashi shawarar ya shigar da Iyayen Gidan Rararan ƙara a gaban Kotu su ma, da su ce musu, su kama sunan Baba Buhari kaitsaye a kalamansu, kamar yadda Mawaƙin ya kira sunansa ya aibata shi, su ga ko zai ƙyale.

Kalaman waɗanda, Alhaji Sani ya yi wa take da ‘Ƙalubale’ na a matsayin martani ne ga mutanen da ke shawartarsa da ya maka Iyayen Gidan Mawaƙi Rarara a gaban Kotu, saboda zargin cewa, Mawaƙin ya isar da saƙonsu ne, ta cikin kalaman da ya furta, ya yin da su ma a wasu lokutan su ke sukar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buharin ta fuskar shaguɓe, ba tare da sun kama sunansa kaitsaye ba.

“Kalubale…….

“Masu cewa inyi karar iyayen gidan Mawakin daya aibata Buhari, kuce masu su kama sunan Baba Buhari su aibata kamar yanda mawaki ya aibata suga ko zan kyale.”, a cewar Alhaji Sani Zangina.

Idan ba a manta ba dai, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya maka Rarara a gaban Babbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa ne, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya jawo tunzuri a tsakanin al’umma, bayan da ya zargi Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da yin dama-dama da ƙasar nan, kafin miƙata ga shugaban ƙasa na yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Alhaji Sani, ya kuma buƙaci kotun da ta bada umarnin tsare Mawaƙin, domin bashi kariya, daga ire-iren barazanar da zai iya fuskanta daga ɗumbin al’ummar ƙasa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button