Al’umma Na Tururuwar Taya Fauziyya D. Sulaiman Murna, Bayan Naɗata A Matsayin Mataimakiya Ta Musamman
Ɗumbin Al’umma, daga ɓangaren Marubuta, Ƴan Siyasa, da ƴan masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), da ma ɗumbin masu amfani da kafafen Sada Zumunta na Zamani (Social Media) ne ke tururuwar aike wa da saƙonnin taya murnarsu ga fitacciyar Marubuciyar nan, da ke Aiki da tashar Talabijin ta Arewa24, Kuma Shugabar Gidauniyar Helping Needy, tun bayan naɗata a matsayin Mataimakiya ta musamman kan tallafawa Mabuƙata da Gajiyayyu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi, a ranar Alhamis, 24 ga watan Augustan da mu ke ciki.
Inda tsananin shauƙi, ya sanya fitacciyar Marubuciyar ta wallafa saƙon godiya, a shafinta na Facebook, a tsakiyar daren ranar Juma’a, ta na mai cewa :
“WACCE IRIN KAUNA AL’UMMA KE MUN?.
“Da farko zan fara mika godiya ga mai girma Gwabnan Kano, His Excellency Abba Kabir Yusuf bisa zaboni da ya yi cikin dubannan mutane ya bani wannan mukami na Senior Sepecial Assistant on Needy and VULNERABLE (Humanitarian) domin gani da kuma yadda da ya yi da ayyukan da muka jima muna yi na taimakawa mabuka, marayu da masu rauni, wanda ya gani da kansa a shafinmu na yanar gizo-gizo.
“Tabbas yau na kara jin dadi bisa wannan aiki da ubangiji ya nufeni da yi, domin lokacin da na je amsar Appointment latter, duk inda muka shiga da an ji sunana sai ace itace wacce mai girma Gwabna jiya ya dauki kusan minti talatin a gurin meeting yana bayaninta, tabbas wannan babban abun alfahari da farin ciki ne gareni, nagode kwarai da gaske ga mai girma Gwabna da masu taimaka masa baki daya.
“A bangaran al’umma kuwa, dukkan godiyar da zan yi ba za ta gamsar dani ba, domin irin soyayya da kauna da suka nuna mun tunda na zo duniya ban taba ganin irin taba, tun ina iya bayar da amsa ga kiran waya da sakon Message da bayar da amsa a social media har na kasa saboda yawan sakonni, daga jiya zuwa yau al’umma sun nuna mun soyayyar da tabbas ban da ubangiji babu wanda zai yiwa dan’adam wannan baiwar, ina godiya da yabo ga ubangiji bisa wannan ni’imar.
“Maganganu na yabo da karfafa gwiwa daga ko’ina, tun ina dariya da murna har na koma yake da tsoro, saboda ganin yadda al’umma suke ganin wani sauki zai zo daga bangarena ta sanadiyyar wannan mukamun da aka bani, sai na koma rokon ubangiji akan ya bani nasara, ya Allah ba zan iya ba ka iya mun, Allah kasa kar na kunyata mai girma Gwabna da al’umma da suke da fata da burina akaina bisa wannan kujera.
“Daga karshe ina kara godiya ga dukkan wadanda suka yi posting ko kirana a waya ko sakon Message ko suka yi addu’a ma kawai, nagode, nagode, nagode, Allah ka ci gaba da ba mu ikon yin komai dominka.
“Fauziyya D. Sulaiman.
Senior Special Assistant to Kano state Governor.”.
Jama’a da dama dai, na ganin wannan muƙami da Gwamnan ya gwangwaje Marubuciyar da shi, a matsayin “Aje ƙwarya a gurbinta”, duba da yadda ta yi shura a wannan fanni na Ayyukan Jinƙai.