Al’umma Sun Ƙosa Su Fara Ganin Kyakykyawan Sauyi – Sarkin Musulmi
Majalissar Ƙoli kan harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta tunasar da shuwagabanni kan jagoranci na gari, tana mai cewar al’ummar Najeriya sun ƙosa su fara ganin sauye-sauye na gari, waɗanda za su sabunta musu ƙwarin guiwoyinsu.
A gefe guda kuma, Sarkin ya buƙaci al’ummar Najeriya da su kasance masu ƙara haɗa kan ƙasa, tare da cigaba da gudanar da ayyukan da za su tabbatar da ita a matsayin ƙasa ɗaya – al’umma ɗaya.
Sultan, wanda shi ne Shugaban Shuwagabannin Gargajiya, ya buƙaci hakan ne, a yayin bikin cikar Sarkin Lafia, Mai Shari’a Sidi Bage-Mohammed, shekaru 17 akan karagar mulki, da ya gudana, ranar Asabar a birnin Lafia.
Sarkin ya tunasar da cewa, akwai matsaloli a kowacce ƙasa, yana mai ƙarawa da cewar, sulhu ba shi ne mafita kan halin rashin tsaron da ya ke tunkarar ƙasar nan ba.
Ka zalika, ya buƙaci Ƴan Najeriya da su kasance masu yi wa shuwagabanni Addu’a wajen ganin sun cimma nasara.
Inda ya buƙaci shuwagabanni a kowanne mataki da su ɗauki matakan shawo kan matsayin tattalin arziƙi da na rashin tsaron da ake fama da shi a ƙasar nan.
Ya kuma bayyana haduwar da shuwagabannin gargajiya su ka yi a jihar, a matsayin wata alama da ke bayyana haɗin kai, inda ya yi kira ga dukkannin ƴan Najeriya da suma su bi makamanciyar hanyar.
A nasa ɓangaren, Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, yi wa shuwagabannin gargajiyar maraba da zuwa jihar ya yi, tare da taya Sarkin murnar shafe shekaru biyar akan mulki.
Inda ya ƙara da jaddada irin goyon bayan da Gwamnatinsa ke bawa shuwagabannin gargajiya, tun bayan zuwanta a shekarar 2019.
Inda ya ƙara da shan alwashin inganta walwalar mazauna jihar.
Manyan baƙin da su ka halarci bikin sun haɗarda: Tsofaffin Gwamnonin jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, Sanata Umaru Tanko Al-Makura; Sarkin Sokoto, Shehun Borno, Oni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II, Aku Uka na Ukari, Sarkin Kano, Sarkin Bauchi, Sarkin Zazzau, Edu Nupe, Lamidon Adamawa, Sarkin Biu, da sauransu.