Zamantakewa

Amarya Ta Bankawa Gidan Angonta Wuta, A Adamawa

An kama wata Amarya mai shekaru 20 a duniya, Amina Alhassan, da ke ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa, a jihar Nasarawa, bisa zarginta da bankawa gidan Angonta wuta.

Rahotanni sun bayyana cewar, Amina ta ɗauki wannan mummunan mataki ne, bayan da Angon nata ya gaza sakinta, kamar yadda ta buƙata.

Ma’auratan dai, sun ƙulla wata yarjejeniya ta musamman ne kafin Auren su.

Tun da farko kuma, Amina ce ta sanar da Iyayenta cewar, bata sha’awar Auren da ake shirin ɗaura mata da sahibin nata, kwanaki kaɗan kafin biki.

Amma Iyayen su ka haƙiƙance kan cewa, wajibi ne a yi bikin, tun da tuni sun raba katinan gayyata.

Bayan Auren ne kuma, sai ta yi yunƙurin haɗa kai da wani Boka, domin ya sa Mijin nata ya tsaneta, har ta kai ga sawwaƙe mata.

Inda bokan ya karɓi Naira 12,000 daga wurinta, a matsayin kuɗin Aiki.

Sai dai, asirin da aka yi, ya ƙara jefawa Amina tsanar Auren nata ne, a madadin Mijin nata ya tsaneta.

Kuma tuni matashiyar Amaryar ta amsa laifinta, bayan da ta shiga komar rundunar ƴan sandan jihar ta Adamawa.

Tuni dai aka fara gudanar da bincike kan lamarin, bisa umarnin Kwamishinan ƴan sandan jihar, Afolabi Babatola.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya rawaito Amina, a ranar Talata ta na cewa, “Mun shirya cewar zai sake ni ne bayan Auren. Na kuma same shi nace ya sake ni kamar yadda ya yi alƙawari, amma ya ƙi”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button