Ƙasashen Ƙetare

Amurka Da Saudiyya Sun Janye Daga Tattaunawar Sulhu, Kan Yaƙin Sudan

Saudi Arabia, Amurka, tare da masu shiga tsakani daga nahiyar Afirka, sun dakatar da tattaunawar da su ke yi da Mayaƙan SAF, tare da gamayyar rundunonin Jamián tsaro na RSF, da ke ƙasar ta Sudan, wacce ke gudana a birnin Jeddah, na Saudi Arabia, har sai abin da hali ya yi.

Kamar yadda rahotannin wasu kafafen yaɗa labarai a ƙasar ta Sudan su ka bayyana.

An kuma dakatar da tattaunawa da ɓangarorin biyu ne sakamakon gaza ɗaukar matakan ƙarawa tawagar sulhun ƙwarin gwuiwa da aka hanga daga ɓangarorin, ba ya ga janye Jamián Sojoji, daga manyan titunan ƙasar.

Zuwa yanzu kuma, gamayyar tawagar masu shiga tsakanin na ƙungiyar haɗa kan ƙasashen Afirka, na Amurka, har ma da na Saudi Arabia, ba su sanar da dakatar da tattaunawar ba, duk da cewar ta ƙare dutse a hannun riga, ba tare da cimma wata tartibiyar matsaya ba.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar 7 ga watan Nuwamban da ya gabata ne, ɓangarorin guda biyu, su ka cimma yarjejeniyar ɗaukar matakan jin ƙan da za su sauƙaƙawa fararen hular ƙasar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button