An Ƙaddamar Da Babban Jirgin Dakon Kayayyaki Irinsa Na Farko, A Najeriya
Ministan sufuri, Saidu Alkali, ya ƙaddamar da jirgin ɗaukar kayayyaki (CARGO) na farko, da zai dinga Aikin jigilar kaya daga Lagos zuwa Ibadan, a ranar Talata.
Ministan ya ƙaddamar da fara aikin jirgin ne a tashar Ebute Meta, kafin kuma ya wuce zuwa Apapa, domin ƙaddamar da wani Aikin, inda ya koma zuwa Ibadan ta hanyar titin jirgin ƙasa mai tsawon kilomita 157.
An kuma yi sawu uku, ɗauke da ƙananan kekunan ɗaukar kaya guda 30 ne, a matsayin mafarin ƙaddamar da jigilar jirgin ɗaukar kayan.
Hukumar kula da Jiragen ƙasa ta NRC, ta bayyana cewar za ta fara ne da yin sawu uku a kowacce rana, kafin cigaba da ƙara adadin a nan gaba.
Shugaban hukumar, ya bayyana cewar, su na sa ran tashar Apapa, za ta mamaye kaso 92.28 na jimillar fitar da kayayyaki, da kuma kaso 60.77 na shigowa da su, ta hanyar amfani da jiragen da hukumar ke samarwa.