An Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Wasannin Paralympics
A jiya ne, Ministan matasa da cigaban wasanni, Sunday Dare, ya rantsar da sabon zababben kwamitin da zai jagoranci farfado da wasannin Paralympic wato wasannin masu bukata ta musamman, dan ganin an cigaba da damawa da su a dukkannin gasannin da ake gudanarwa.
Da ya ke jawabi, a ya yin rantsarwar, wacce ta gudana a budadden filin wasa na Steven Keshi, da ke Asaba, a jihar Delta, Ministan ya bayyana matukar jindadinsa game da sababbin shuwagabannin da aka zaba, ya na mai bada tabbacin cewar kasar nan zata farfado daga koma bayan da ta samu, a fagen wasannin na Paralympics, a nan gaba.
A cewar sa dai, wasannin na Para-Sports na daga cikin wasannin da ke daga kimar kasa a idon duniya, musamman akan alámuran da ke da jibi da wasanni.
Inda kuma ya yi kira ga membobi da shuwagabannin sabon kwamitin da su yin amfani da dukkannin kwarewarsu, da ma Ilimi wajen gudanar da ayyukan kwamitin bisa tsari, da ma inganta wasannin Para-Sports a kasar nan.
Da ya ke taya sababbin membobin kwamitin murn kan zabarsu da aka yi, ya kuma godewa Gwamnatin jihar Delta bisa amincewa r da ta yi da karbar bakuncin taron kaddamarwar. Da ya ke martani ga jawabin Ministan, sabon zababben shugaban kwamitin na PCN, Mr. Odebode Sunday, ya sha alwashin cicciba kasar nan a fagen wasannin masu bukata ta musamman, kafin karewar zangon shugabancinsu. Sababbin zababbun shuwagabannin kwamitin na PCN dai, sun hadar da Odebode Sunday a matsayin shugaba; Shodipo Ayinde a matsayin mataimakiyar shugaba ta farkó; Ungwunwa Flora a matsayin ta biyu, kuma wakiliyar yan wasa mata; da ma Isah Suleiman da ke matsayin Babban Sakatare.