An Ƙaddamar Da Sabon Kakin NSCDC
A jiya (Alhamis) ne, Ministan cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya ƙaddamar da sababbin kayan Jami’an hukumar NSCDC mai roɗi-roɗi.
Wani jawabi da mai magana da yawun ma’aikatar cikin gidan, Afonja Ajibola ya fitar, ya bayyana yadda ministan ya yi alƙawarin cewar, Gwamnati za ta cigaba da tallafawa hukumar ta Civil Defence, tare da bata goyon baya wajen tabbatar da walwalar Jami’anta.
Ministan ya kuma ce, sabon Uniform ɗin Jami’an hukumar da aka ƙaddamar, zai ƙarawa Jami’an karsashi a cikin aikin da su ke gudanarwa na tsaro.
A jawabinsa tun da farko, Kwamanda Janar na hukumar ta NSCDC, Abubakar Audi, ya bayyanawa Ministan cewar, Jami’an hukumar su na bada gagarumar gudunmawarsu a dukkannin ayyukan haɗakar da ya haɗa da su, duk kuwa da basu da samfurin kayan mai roɗi-roɗi.
Inda ya ce sababbin kayan za su ƙarawa Jami’an su ƙwarin guiwa a ya yin da su ke gudanar da ayyuka, domin kuwa samfurin kayan mai roɗi-roɗi zai sanya su yi kamanceceniya da takwarorinsu.