Ilimi

An Ƙara Hutun Makarantun Firamare Da Sakandire A Kaduna

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kaduna, ta sanar da ƙara hutun makaranta ga Ɗaliban Makarantun Firamare da Sakandiren Jihar, zuwa ranar Lahadi, 24 ga watan Satumbar da mu ke ciki, ga Ɗaliban Makarantun Kwana, da kuma 25 ga watan na Satumba ga Ɗaliban Makarantun Je Ka Ka Dawo (Day).

Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan ma’aikatar Ilimin Jihar ya fitar, mai ɗauke da sa hannun, Babban Sakataren Ma’aikatar, Dr. Halliru Musa Soba, wacce kuma ke ɗauke da kwanan watan, 08 ga watan Satumban 2023, wacce kuma aka aike ga dukkannin Shuwagabannin Makarantun Firamare da Sakandiren Jihar, tare da Shugaban ƙungiyar Iyayen Yara da Malamai (PTA), da Shugaban NAPPS na Kaduna, da ma dukkannin Makarantu masu zaman kansu, da na sa kai, Sai Shugaban ANCOPSS na Kaduna, da Shugaban Kwamitin SBMC, da ma Shugaban ƙungiyar Malamai (NUT) reshen Jihar ta Kaduna.

Sanarwar ta kuma buƙaci Iyaye da sauran masu kula da yara da su kiyaye da wannan sabuwar rana, ta na mai cewar, za a saki sabuwar kalandar karatu wacce ke ɗauke da ɗagawar da aka yi, a nan kusa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button