Zamantakewa
An Ƙwace Sama Da Kura 300 A Legas, Saboda Zubar Da Shara Ba Bisa Ƙa’idaba
Hukumar kare gurɓatar muhalli ta jihar Lagos (LAWMA), ta ƙwace sama da kura mai ƙafa uku (Wheelbarrow) guda 300, bayan samun su da laifin zubar da shara ba a wuraren da aka tanada ba.
Hotunan yadda aka ƙwace kurar har sama da guda 300 dai, an wallafa su ne, a shafin hukumar ta LAWMA, da ke kafar sada zumunta ta X, a ranar Lahadi.
Inda hukumar ta wallafa, “Zubar Da Shara Ba Bisa Ƙa’idaba: Kwamitin karta kwana na hukumar LAWMA, ya samu nasarar ƙwace sama da kura mai ƙafa uku guda 300 daga matuƙansu, bayan samun su da laifukan zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, akan hanyar Lekki Epe Expressway. Hakan kuma laifi ne da ya ci karo da dokokin kula da muhalli na jiha”.