An Ɗage Gasar Ƙwallon Ƙafar Mata Ta Ƙasa
A ranar Talata ne, masu alhakin shirya gasar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasa, su ka tabbatar da cewar, an umarce su da su ɗage lokacin gudanar da gasar wacce ke ƙara ƙaratowa, ta zaratan ƙungiyoyi 6.
Sai dai jawabin nasu bai bayyana dalilin aiwatar da hakan ba.
Tun da farko, an tsara gudanar da gasar ne dai, a birnin Asaba, na jihar Delta, a tsakanin 5 zuwa 12 ga watan Mayu.
Ƙungiyoyi shidan da za su ɓarje gumi a gasar sun haɗar da Delta Queens, Rivers Angels, da masu riƙe da kambun gasar Bayelsa Queens, Confluence Queens, Robo Queens da kuma Edo Queens.
Modupe Shabi, wadda ke zama babbar jami’ar gudanarwar gasar, ita ce ta tabbatar da ɗage gudanar da gasar, ta cikin wani jawabi da ta fitar, a ranar Talata, 2 ga watan Mayu.
Ta kuma ce, za a yanke hukunci kan sabuwar ranar gudanar da gasar da za a sanya, bayan kammala gudanar da gasar ƙwallon ƙafar mata ƴan ƙasa da shekaru 20 ta duniya, da za a yi a birnin Kumasi, na ƙasar Ghana, daga ranar 20 ga watan Mayu, zuwa 3 ga watan Yuni.