An Ɗage Lokacin Sake Gurfanar Da Ɗanbilki Kwamanda A Gaban Kotu
Rashin zuwan Alƙalin Kotun Majistiri, Abdulaziz Habib Kotu, a ranar Litinin, ya kawo tsaiko kan shari’ar da fitaccen ɗan siyasar nan, Abdulmajid Ɗanbilki Kwamanda ya ke fuskanta a gabanta, bisa zarginsa da yunƙurin tada zaune tsaye, ya yin tattaunawarsa da wata kafar yaɗa labarai, ta Rediyo.
Laifin da ake zargin Ɗanbilkin dai, ya saɓa da sashe na 114, na dokokin Penal Code.
Hakan kuma ya kawo cikas, ga buƙatar bayar da shi beli, da Lauyan da ke bashi kariya, Ibrahim Abdullahi-Chedi, ya shigar, a gaban Kotun.
Lauyan ya buƙaci Kotun da ta damƙa wanda ya ke karewa a hannun beli, dogaro da sashe na 35(5), da sashe na 36 na kwaskwararren daftarin kundin dokokin ƙasar nan, na shekarar 1999.
Rashin lafiyar da Alƙalin Kotun ke fuskanta kuma, ya tilasta ɗage cigaba da sauraron shari’ar, zuwa ranar 1 ga watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki.
Mai gabatar da ƙara, Abdussalam Saleh, ya zargi wanda ake ƙarar da yunƙurin tada husuma kan batun shirin gwamnatin Kano, na sake fuskantar sha’anin Masarautun jihar, ya yin wata tattaunawa da ya gudanar, a gidan rediyo, a cikin watan Janairun da mu ke ciki.
Sai dai, Ɗanbilkin ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.