An Ɗaure Ɗaliba Shekaru 6 Saboda Satar Waya, A Borno
Kotun Majistiri, da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno, ta ɗaure wata Ɗaliba mai suna, Balkisu Baba Shehu tsawon shekaru shida, a gidan gyaran hali, bayan samunta da laifin satar waya.
Tun da farko dai, Ɗan Sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Jarus Manu, ya bayyana wa Kotun cewar, wata Matashiya mai shekaru 27, Mercy Babayo ce, ta shigar da ƙarar Balkisu Baba Shehu ɗin, wacce ƙawarta ce a ofishin rundunar ƴan sanda, da ke Gwange, bisa zarginta da sace mata waya ƙirar Infinix Hot 12, wacce ƙimarta ta kai Naira 70,000, wacce ta ke zargin ta yi mata sama da faɗi da ita ne, ya yin da ta ajiyeta a cikin Jakarta, bayan zuwansu kasuwa tare, a ranar Litinin.
Bayan isar su gida daga kasuwar ne kuma, sai Mercy ɗin ta fahimci cewa, ba ta ga wayarta a cikin jakar ba, duk da cewar wayoyi biyu ne a cikin jakar, amma ta Mercy ɗin ta yi ɓatan dabo.
Bayan karantawa wacce ake zargin laifinta ne kuma, sai ta amsa nan ta ke.
Inda Alƙalin Kotun, Alhaji Saleh Isa, ya yanke wa matashiyar Ɗalibar hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan gyaran hali, ko zaɓin biyan tarar Naira 100,000 tare da kuɗin wayar Naira 70,000.