An Ɗaure Likita Tsawon Watanni 12, Saboda Kashe Saniyar Maƙwabcinsa
A ranar Alhamis ne, Kotun Majistiri, da ke jihar Ogun, ta yankewa wani Likita mai shekaru 45, Michael Oyewole, hukuncin zaman gidan gyaran hali, na tsawon watanni 12, bayan samunsa da laifin kashe saniyar maƙocinsa.
Tun da farko, mai ƙara wanda ke zaune a yankin, Araromi Alakaloko Olomore, na jihar Abeokuta ne dai, ya shigar da Likitan ƙara a gaban Kotu, bisa zarge-zarge guda uku na na cin amana, sata, tare da kashe masa saniya ba bisa ƙa’ida ba.
Bayan sauraron ƙarar ne kuma, sai Alƙaliyar Kotun, Mai Shari’a O O Odumosu ta tabbatar da cewa, wanda ake ƙarar ya aikata laifukan da ake zarginsa da su, sakamakon tarin hujjojin da aka gabatar mata.
Inda ta yankewa Likitan hukuncin ɗaurin watanni 12 a gidan gyaran hali, ko zaɓin biyan tarar Naira 10,000, sai dai Likitan zai bada waccar 10,000 ne, bayan ya biya mai ƙarar Naira 400,000 kuɗin saniyarsa da ya kashe.
Kafin yanke hukuncin dai, Ɗan Sanda mai gabatar da ƙara, ASP Olakunle Shonibare, ya bayyanawa Kotun cewar, a ranar 3 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 11 na dare, wanda ake ƙarar, ya haɗa kai da wasu mutane, a unguwar Alakaloko Unique, da ke yankin Olomore, na jihar Abeokuta, inda su ka sace Saniyar mai ƙara, Hakeem Ominrinde, wacce kimarta ta kai Naira 400,000.