Ƙasashen Ƙetare

An Ɗaure Tsohon Shugaban Ƙasar Mauritania, Tsawon Shekaru 5 Bayan Samunsa Da Laifin Aikata Rashawa

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne, Kotun Nouakchott, wanda shi ne babban birnin Mauritania, ta ɗaure tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Ould Abdel Aziz tsawon shekaru biyar, bayan samunsa da laifin aikata almundahana, a lokacin da ludayinsa ke kan damo.

Aziz, ya jagoranci ƙasar, wacce ke yankin Arewacin Afirka ne, daga shekarar 2008 zuwa 2019, inda kuma ya fuskanci tuhumar aikata rashawa bayan saukarsa daga kujerar shugabancin ƙasar, daga sabon shugabanta na yanzu, Mohamed Ould Ghazouani.

An dai fara tuhumar tsohon shugaban ƙasar tare da waɗansu mutane 10 ne, tun a watan Janairun shekarar da mu ke ciki.

Sauran waɗanda aka tuhume su a tare, sun haɗarda Tsofaffin Fira Ministocin ƙasar guda biyu, waɗanda aka zarga da laifin azurta kai.

Sai dai, daga bisani Kotun ta wanke dukkannin sauran ɓangarorin.

Kotun ta kuma tabbatar da cewar, Aziz ɗin ya mallaki wasu kadarori ba bisa ƙa’ida ba.

Zuwa yanzu kuma, tsohon shugaban mai shekaru 66 a duniya, bai ce ko uffan game da hukuncin da Kotun ta zartar ba.

Aziz dai, ya kasance a tsare, tun ranar 24 ga watan Janairu, bayan shafe tsawon watanni a gidan ajiya da gyaran hali tun shekarar 2021.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button