Kasuwanci
An Buɗe Shafin Neman Tallafi Ga Masu Sana’o’in Hannu
Gwamnatin tarayya, ta bude dama ga mutanen da ke gudanar da ayyukan hannu, masu bada horo, da wadanda su ke gudanar da sana’o’in da ke da alaka da fasaha, na neman tallafin Naira dubu 500 da gwamnatin za ta bayar.
Wani jawabi da hukumar wayar da kan al’umma ta fitar, a ranar Litinin, ya bayyana cewar, shirin bada tallafin na daga cikin yunkurin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ke yi, na farfado da fannin fasaha, tare da cibiyoyin da ke bada horo kan sana’o’in dogaro da kai.
Jawabin, ya kuma kara da cewar, an samar da tallafin ne, dan tabbatar da tsayawar Najeriya da kafarta ta fuskar sana’o’in dogaro da kai, tare da karfafar dai-daikun mutane dan su dogara da kansu.