Ilimi

An Buɗe Shafin Neman Tallafin Karatu A Ƙasar Burtaniya

An buɗe shafin neman tallafin yin karatu, na Chevening, a Burtaniya, a ranar Talata, 12 ga watan Satumban 2023, kamar yadda Babban Sashen Jakadancin Burtaniya a Najeriya ya bayyana.

Tallafin karatun wanda za a rufe damar nemansa, a ranar 7 ga watan Nuwamban 2023, ana cike shi ne ta kafar Intanet, a adireshin chevening.org/apply.

Damar neman wannan tallafin karatu kuma ta zo ne, bayan zaɓar ƴan Najeriya kimanin 44, waɗanda suka samu sahalewar yin karatu a Jami’ar ƙasar ta Burtaniya, a wannan shekarar.

Inda waɗanda su ka samu tallafin su ka dinga bayyana bayanin samun nasararsu ta hanyar amfani da hashtag na #ChosenForChevening, a kafafen sadarwar zamani na Twitter da Instagram.

Shugabar sashen tallafin karatu a Burtaniya, da ma ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Commonwealth, Emma Hennassey, ta ce, “Tallafin Karatu na Chevening, na bawa ɗaliban da su ka amfana damar yin amfani da dabarun da su ka koya, ya yin da su ke karatu a Turai ɗin, wajen kawo sauyi, ciyar da Al’umma gaba, da ma haɓɓaka Ayyuka a faɗin Duniya”.

Shugabar ta kuma bayyana cewar, zuwa yanzu akwai aƙalla tsofaffin Ɗalibai 55,000 da su ka amfana da wannan tallafi.

A nasa ɓangaren, Babban Kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery, ya ce: “Idan kun san wani Mutum da ya ke da ra’ayin kawo sauyi, a ƙaramin yanki ko a matakin duniya, to tsarin tallafin karatun Chevening, babbar dama ce a gare shi.

“Babu ruwanmu da waye mutum. Domin shekarunka, Girmanka, Jinsinka, Addininka, da ma Al’adar mutanen da ka fito dukka bai damemu ba. Muna son kawai mu ga kana da mayar da hankali akan gina gobenka ne, tare da cimma nasarori”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button