Labarai

An Buɗe Tashar Lantarki Ta Afam

A ranar Talata ne, Shugababan kasa Muhammadu Buhari, ya bude aikin wutar lantarki ta Afam, da zai din ga samar da megawatts 240, a yankin Okoloma Afam, da ke karamar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers.

Shugaban, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, a wurin bude gidan wutar, ya ce cibiyar hasken lantarkin ta Afam 3, ta na daga cikin muhimman yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi, wajen habbaka samar da wutar lantarki, ga miliyoyin gidajen yan Najeriya, da ma habbaka kasuwancinsu, dan ganin alúmma sun rayu cikin walwala. Ya kuma ce samar da wutar zai taka muhimmiyar rawa wajen habbakar sanya hannayen jari, duba da cewar rashin wutar ne ke cigaba da kasancewa babban kalubalen fannin.

A nasa bangaren, shi ma Ministan makamashi, Injiniya Abubakar Aliyu, wanda ya samu wakilcin babbar sakatariyar maáikatar, Temitope Fashedemi, ya ce samar da aikin guda ne daga cikin nasarorin da gwamnatin tarayya ta cimma a fannin makamashi, kuma na daga cikin yunkurin da ta ke yi na ganin an kawo karshen tazarar da aka iwa Najeriyar a fannin wutar lantarki.

Ya kuma ce alúmmar kasar nan sun san muhimmancin da fannin wutar lantarkin ke da shi, kuma kowanne daga ciki yasan illar rashinta, a fannonin zamantakewa, kasuwanci, karatu, da ma a Cibiyoyin kula da lafiya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button