An Cika Hannu Da Kwamishinan Ƴan Sandan Bogi, A Lagos
An kama Kwamishinan ƴan sanda na bogi, a jihar Lagos, bayan da ya kutsa kai cikin ofishin rundunar ƴan sanda, ya kuma buƙaci a saki wani mutum da ake zargi da aikata laifi.
Emmanuel Nwagu, mai shekaru 60 a duniya ya sha sarawar ban girma, bayan da ya shiga Ofishin rundunar, kafin ƙwaƙwƙwaran bincike ya tabbatar da cewar kawai ya na Sojan Gona ne da muƙamin.
A ya yin da ya ke holin wanda ake zargin, da wasu mutane 13, a ranar Litinin, Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta Lagos, Ben Hundeyin, ya ce Ƴan Sanda sun yi bincike a gidan Nwagu ɗin bayan daƙume shi, inda su ka sake yin arba da wasu kayayyakin na Aikin ƴan sanda.
“An samu Katin shaida na Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda, Kayan Sawa na Jami’an Ƴan Sanda, Singlet ɗinsu da Hularsu ƙirar Facing Cap,” a cewar Hundeyin.
Kakakin ya kuma yi ƙarin bayani kan yadda hukumarsu ta samu nasarar cika hannunta da Kwamishinan.
“Ya shigo Ofishin ƴan sanda, ya kuma gabatar da kansa a matsayin Kwamishina, Sannan ya ce, akwai wani mutum da ake zargi, Wanda nake son a saki…”, A cewar Hundeyin ɗin.
Da aka tambaye shi ko ya aka yi Kwamishinan ya mallaki takardar izinin saki ?, Sai Hundeyin ya ce, “Ya yi iƙirarin cewar Jami’in ɗan sanda daga Ofishin Lagos ne ya bashi, sai dai sunan da ya ke bayarwa akwai sarƙaƙiya a cikinsa, domin kuwa an gaza gane wanne Jami’i ne, a kundin adana bayanan hukumar ƴan sanda.
“Ta yiwu gaskiya ya ke faɗa kan cewar Jami’in ɗan sandan ne ya bashi, ko kuma ƙarya ya yi game da sunan Jami’in. Ban sani ba, ko muna da shaidar da zamu iya tsare shi”.
Ko a ranar Litinin, 4 ga watan Satumban da mu ke ciki ma dai, sai da rundunar ƴan sanda ta yi ram da wani Mai yin Sojin Gonan, bayan da ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa, NBA, reshen Epe ta gabatar da ƙorafi akansa.
NBA ɗin kuma, ta shigar da ƙarafi ne, kan wani mutum mai suna Bello, Wanda ke bayyana kansa a matsayin Lauya, har tsawon shekaru bakwai, a Babbar Kotun Majistiri, da ke Epe.