An Daƙume Limamin Coci, Bisa Zargin Damfarar Wata Mata
Rundunar tsaro mai bada kariya ga fararen hula, NSCDC, ta samu nasarar daƙume wani Pastor mai shakaru 39 a duniya, Michael Ogundepo, a jihar Ondo, bisa zarginsa da damfarar wata Mata, mai suna, Miss Fagbuyiro Ajetomobi, zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 1.6.
Kakakin rundunar ta NSCDC, reshen jihar, Daniel Aidamenbor, wanda ya tabbatar da kama Limamin Cocin, ya ce ana zarginsa ne da karɓar Littafin tafiye-tafiye (Passport) mallakin, Miss Fagbuyiro Ajetomobi, tare da karkatar da kuɗaɗenta zuwa biyan buƙatar ƙashin kai, inda hakan ya hanata damar mallakar Visa.
Ga abin da jawabin ya ke cewa, “An kama, Michael Ogundepo, mai shakaru 39, wanda kuma Limami ne a Cocin da ke Lamba 15 Layin Ewu Agbo, Ikorodu, Lagos, kan laifin damfarar, Miss Fagbuyiro Ajetomobi Yemi, da ke zaune a gida mai lamba 110 Osi Igoba, Akure, bayan da ya fake da cewar zai taimaketa, wajen samun Visa, inda ya karkatar mata da zunzurutun kuɗi har Naira 1,670,000.
“Rundunar mu, ta gayyaci wanda ake zargin sama da sau shurin masaƙi, amma ya sa ƙafa ya shure wannan gayyata, ta hanyar ƙin zuwa. Inda ya yi iƙirarin cewar ba ya ƙasar nan, har ma ya yi amfani da lambar ƙasar waje ta bogi, ya kira mai ƙarar.
“Mun kuma kama wanda ake zargin ne, bayan da aka gayyace shi ya karɓi kuɗi Naira 3,000,000 domin yin Aikin Visa, ba tare da ya san abin shiri bane”.
Aidamenbor, ya ce binciken da jami’an hukumar su ka gudanar, ya gano cewar, wanda ake zargin ya damfari mutane da dama.