An Daƙume Mai Gadin Makaranta Bisa Zargin Runtuma Sata
Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, sun kama wani maigadi, Hassan Adamu, bisa zarginsa da sace na’urar ɗab’i (Printer), da ma ƙananan na’urori masu ƙwaƙwalwa guda biyu, fankokin sili biyu, da ma Disc Receiver, a makarantar Sakandiren Gwamnati ta haɗaka da ke ƙaramar hukumar Kazaure.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, shi ne ya bayyana hakan, ta cikin wani jawabi da ya fitar, ranar Juma’a, a birnin Dutse.
Shiisu, ya ce Mataimakin Shugaban Makarantar ne ya kai rahoton runtuma satar, ga rundunar ƴan sanda, ya yin da ya ankara da rasa kayayyakin.
Bayan karɓar rahoton ƙorafin nasa ne kuma, sai rundunar ta tashi wata tawaga ta musamman a ofishinta na Kazaure, inda su ka mamaye wani shagon sayar da kayayyaki da ke unguwar Kan Gada, a ƙaramar hukumar ta Kazaure, inda su ka yi nasarar daƙume wanda ake zargin ɗauke da Printer guda, ƙananan Kwamfutoci biyu, Fankokin sama guda biyu, da ma Disc Receiver ɗaya.
Jawabin dai na cewa, “a ranar 19 ga watan Satumba, Bashir Ahmed, mai shekaru 50, da ke matsayin Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandiren Ƴan Mata Ta Haɗaka, da ke Kazaure, ya kai rahoto Ofishin rundunar ƴan sandan ƙaramar hukumar, inda ya ce, a ranar 18 ga watan Satumban 2023, da misalin ƙarfe 17:00 na yammaci, ya gano cewar, wasu mutane da ba a san ko su waye ba, sun wawashe wasu daga cikin kayayyakin makarantar.
“Bayan tsaurara bincike kuma, sai mu ka gano cewar, mutumin ya yi amfani da Master Key ne, wajen buɗe ɗakin ajiyar kayayyakin makarantar, inda ya yi awon gaba da wasu daga cikin kayayyakinta.
“Kuma Jami’an binciken rundunar mu, sun halarci wurin da lamarin ya faru, tare da gano makullin na Master Key”, a cewarsa.
Kakakin, ya kuma ce, Mataimakin Shugaban Makarantar ya gane kayayyakin, bayan da aka gano su, inda ya ce har yanzu dai, babu wasu abubuwan.
Ya kuma ce, za su gurfanar da Wanda ake zargin a gaban Kuliya, domin girbar abinda ya shuka.