An Daƙume Malamin Jami’a Bisa Zargin Yi wa Ɗalibarsa Aika-Aika
Rundunar ƴan sanda, ta kama wani Malamin Jami’ar Lagos (UNILAG), Kadiri Babalola, bisa zarginsa da yi wa wata ɗalibarsa mai shekaru 20, da ke karatun Digirin farko, a makarantar fyaɗe.
Ɗalibar da aka yi wa Aika-Aikar, ta zargi Babalola da ke matsayin Associate Professor, a fannin nazarin tsirrai (Botany), da take dokar da ta haramtawa Malamai kusantar ɗalibansu, a ranar 16 ga watan Augustan da ya gabata, bayan da ta halarci Ofishinsa, da nufin yin gyara kan wata matsala da ta shafi sakamakon Jarrabawarta.
Tuni kuma Jami’an ƴan sanda, su ka cika hannunsu da wannan Malami, bayan da wata gidauniyar kare ƴancin mata, da bunƙasa walwalarsu ta shigar da ƙorafi akansa, a Ofishin rundunar da ke Ikeja, jim kaɗan bayan kwarmata batun da Ɗalibar ta yi.
Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama wannan Malami, bisa zargin cin zarafin Ɗalibarsa, inda ya ce za a gurfanar da shi a gaban Kuliya, da zarar an sanya lokaci.
A nasa ɓangaren, wani Malami a Jami’ar (wanda lamarin bai shafa ba) ya bayyana kaɗuwa da rashin jindaɗinsa matuƙa bisa aukuwar wannan lamari.
“Ba mu taɓa tsammanin hakan ba, saboda Babalola mutum ne mai ƙwazo, da kima a Idon Al’umma”, a cewar Malamin.
A nata ɓangaren Shugabar Gidauniyar InclusiveSWEF, Pat Isiorho-Eleto, ta ce za su cigaba da bibiyar sha’anin, duk da cewar za a ɓoye bayanan ɗalibar da abin ya rutsa da ita.
A nasa ɓangaren, Mai Magana da yawun Makarantar, Adejoke Alaga-Ibrahim, ya ce Jami’ar na sanya Ido kan binciken da ake gudanarwa.
Inda ya ce, ko a ranar 28 ga watan Augustan da ya gabata ma, sai da rundunar ƴan sanda ta aike da wasiƙar neman ganin wasu daga cikin Ma’aikatan Jami’ar, domin su amsa tambayoyi.
Ya kuma ƙara da bayyana ƙoƙarin Jami’ar na ganin an tabbatar da Adalci a cikin wannan turka-turka.