Nishaɗi

An Dakatar Da Jaruma Khadija Mai Numfashi Daga Kannywood

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, ƙarƙashin Jagorancin babban Sakatarenta, Abba El-Mustapha, ta dakatar da fitacciyar Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Khadija Mai Numfashi, daga fitowa a fina-finai har tsawon shekaru biyu.

Hukumar ta dakatar da Jarumar ne, bayan da ta gaza amsa kiran da aka yi mata, domin kare kanta, bisa zargin tiƙa rawa, irinta waɗanda su ka rasa mafaɗi.

Dakatar da itan kuma, na nufin daga yanzu, babu damar ta fito a cikin fina-finai ko waƙoƙin masana’antar, ka zalika haramun ne ta yi amfani da sunan masana’antar ta Kannywood a dukkannin wani sha’ani da ya shafeta.

Idan ba a manta ba dai, ko a makon da ya gabata ma, sai da hukumar ta dakatar da Jarumi Abdul-Saheer, wanda aka fi sani da Malam Ali, daga fitowa a fina-finai tsawon shekaru biyu, bisa zarginsa da wallafa wani bidiyon batsa, a shafinsa na TikTok.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button