Ilimi

An Dakatar Da Malamin Da Ya Bawa Ɗalibai Horo Mai Tsanani A Jami’ar Wudil

Jami’ar Kimiyya Da Fasaha, ta Aliko Dangote, da ke garin Wudil, a jihar Kano, ta dakatar da guda daga cikin Malamanta, bayan da wani bidiyo, da ke cigaba da karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda Malamin ke bawa wasu daga cikin Ɗalibansa horo samfurin gwale-gwale, bayan da ya zarge su da makara, tare da yin surutu ya yin da ya ke cikin aji.

Jami’ar dai, ta bayyana ɗaukar wannan mataki na dakatar da Malamin, tare da gurfanar da shi a gaban kwamitin ladabtarwarta ne, ta cikin wata sanarwa da Mataimakin Magatakardan Jami’ar na sashen yaɗa labarai, Sa’idu Abdullahi Nayaya ya fitar, da yammacin ranar Talata, 6 ga watan Fabrairun da mu ke ciki.

Sanarwar ta kuma ƙara da buƙatar Iyaye da su kwantar da hankulansu, domin kuwa ƴaƴayensu su na cikin kwanciyar hankali.

Bidiyon Malamin, wanda ke koyar da darasin GST ga ɗaliban aji biyu (Level 200) a Jami’ar dai, ya karaɗe kafafen sada zumunta na zamani, inda al’umma da dama ke cigaba da tofa Albarkacin bakunansu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button