An Dakatar Da Membobin Majalissar Dokokin Zamfara 8
Majalissar Dokokin Jihar Zamfara, ta dakatar da membobin majalissar guda takwas, bayan samunsu da laifin gabatar da zama ba bisa ƙa’ida ba.
Sanarwar dakatar da membobin takwas, ta fito ne ta bakin shugaban Majalissar, Bilyaminu Moriki, ya yin zaman majalissar da ya gudana ranar Litinin, a birnin Gusau.
Dakatarwar kuma ta biyo bayan ƙudirin da shugaban masu rinjaye na majalissar, Bello Mazawaje, na jam’iyyar PDP daga ƙaramar hukumar Tsafe Ta Gabas ya gabatar.
Mazawaje, ya ce dakatar da membobin dama ce da Order 10, Rule 9 ta Majalissar ta bawa membobinta.
Ya kuma ce, membobin da aka dakatar ɗin sun karya ƙofar majalissar a ranar Alhamis, ba ya ga haramtaccen zama da su ka gudanar.
Membobin da aka dakatar sun haɗar da: Bashir Aliyu, na jam’iyyar PDP daga Gummi 1; Amiru Keta, na jam’iyyar PDP daga Tsafe Ta Yamma; Nasiru Abdullahi, na jam’iyyar PDP daga Maru ta Kudu; Bashir Musama, ba jam’iyyar PDP daga Bukkuyum ta Arewa; Faruku Dosara, na jam’iyyar APC daga Muradun 1; Ibrahim Tukur, na jam’iyyar APC daga Bakura; Shamsudeen Hassan, na jam’iyyar APC daga Talata Mafara Ta Arewa; da Bashiru Sarkin-Zango, ba jam’iyyar PDP daga Bungudu ta Yamma.