Ilimi

AN FARA CIRE POST-UTME EXAM CARD, NA JAMI’AR YUSUF MAITAMA SULE, KANO

A yanzu ɗalibai za su iya halartar shafin rijistar Post-UTME na Jami’ar, su kuma sanya Registration Numbers ɗinsu, tare da danna Continue, sannan su danna zaɓin DOWNLOAD ko PRINT, da ke ƙasan maɓullin EXAM CARD, domin cire Katin Jarrabawar su.

Cire Exam Card ɗin zai basu damar sanin Rana, Lokaci, da ma wurin da za su rubuta jarrabawar ta Post-UTME.

KU SANI: Waɗanda su ka yi rijista bayan Makaranta ta ƙara lokaci su ne za su ga actual date na Post-UTME ɗinsu.

Waɗanda kuma su ka yi rijista tun wuri, su jira Makaranta za ta sauya musu ranaku.

📌Za kuma a fara rubuta jarrabawar ta Post-UTME, a ranar Laraba, 13 ga watan September📌

ALLAH YA BADA NASARA.

 

✍️ MIFTAHU AHMAD PANDA

08039411956.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button