Kasuwanci

An Fara Garaɓasar Jumia Black Friday

Fitacciyar kasuwar sayen kayayyaki ta yanar gizon nan, ta Jumia, ta sanar da zaftare farashin kayayyakin da ake iya saya a kasuwar.

Rage farashin da kaso mai tsoka kuma, ya zo ne, ya yin da kasuwar ke bikin bajakolin garaɓasar nan na Black Friday, wanda ta saba gudanarwa a duk shekara.

A wannan shekarar kuma, garaɓasar ta fara ne, daga yau Juma’a, 3 ga watan Nuwamba, zuwa 30 ga watan na Nuwamba.

Dukkannin jama’ar da ke da sha’awar cin moriyar wannan garaɓasa, su na iya sauke Manhajar Kasuwar ta Jumia su kuma yi rijista, ka zalika su na iya yin hakan ta hanyar garzayawa shafin yanar gizon kasuwar.

Kasuwar ta zabge farashin wasu daga cikin kayayyakinta da kaso 80, ya yin da wasu kuwa ta rage farashin su da kaso 99.

Bayan kun yi rijista, za ku ci moriyar tsarin ne, ta hanyar latsa maɓulli da ke ɗauke da hotunan Black Friday, wanda za ku gani daga saman shafin yanar gizon kasuwar, ko Manhajarta.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button