Kotu
An Fara Karanta Hukuncin Zaɓen Gwamnan Kano Ta Allon Gani-Gaka
Alƙalan Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano, sun fara karanta Hukuncin shari’ar zaɓen ta Allon Gani-Gaka (Manhajar Zoom) bayan da su ka gaza halartar Kotun.
Lauyoyi, tare da wakilan jam’iyyu da Ƴan Jaridu ne dai su ka yi dandazo a cikin Kotun, inda su ke kallon hukuncin wanda ake karantawa kaitsaye.
Zuwa yanzu babu masaniyar tartibin dalilin da ya hana Alƙalan Kotun halartar zaman shari’ar a zahiri, sai dai ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da barazanar da Alƙalan su ke ganin za su iya fuskanta, bayan zartar da hukuncin.
Tun da safiyar yau ne dai, Jami’an tsaro su ka yi wa Kotun ƙawanya, tare da rufe hanyoyin halartarta, da nufin rage cunkuson Jama’a, da ma inganta tsaro a farfajiyar Kotun.