AN FARA RIJISTAR NECO (COMMON ENTRANCE DA GIFTED)
Hukumar shirya jarrabawa ta NECO, ta sanar da fara rijistar Jarrabawar Shiga Makarantun Sakandiren Haɗaka Na Tarayya (Federal Government Unity Colleges – COMMON ENTRANCE) da Jarrabawar shiga Makarantar Tarayya Ta Suleja (Federal Government Academy, Suleja – GIFTED).
BAYANI KAN RIJISTA:
Ana rijistar dukkannin jarrabawoyin ne (NCEE ko GIFTED) akan Naira 4,750.00 kan kowanne ɗalibi guda, ana kuma sanya kuɗin ne a ofishin haɗaka na hukumar NECO.
Ana rijista, tare da shigar da bayanan ɗalibi ne kuma, a shafin hukumar NECO, da ke adireshin: www.neco.gov.ng
LOKACIN RUFE RIJISTA
Za a rufe rijistar tagwayen jarrabawoyin ne, da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar fara jarrabawa.
LOKACIN RUBUTA JARRABAWA
Common Entrance – 20 Ga Watan Afrilun 2024.
Gifted – 4 Ga Watan Mayun 2024.
DOMIN ƘARIN BAYANI : 08039411956
Rubutawa : Miftahu Ahmad Panda.
08039411956