An Fara Tura Saƙon Jarrabawa Ga Masu Neman Aikin Ƴan Sanda
Hukumar ƴan sanda ta ƙasa (PSC), ta bayyana cewar tuni aka fara aikewa da saƙon gayyatar rubuta Jarrabawar Na’ura Mai Ƙwaƙwalwa (CBT) ga matasa kimanin 171,956 da su ka samu nasarar tsallake tantancewar Ido da Ido (Physical Screening) da hukumar ta gudanar ga waɗanda ke sha’awar aiki da ita.
Hukumar ta kuma bayyana cewar, za a gudanar da Jarrabawar ta CBT ne, a ranakun Talata da Laraba, 2 da 6 ga watan gobe na Maris, a ɗaukacin jihohin ƙasar nan, guda 36 da babban birnin tarayya Abuja.
Bayanin hakan kuma, ya fito ne, ta bakin mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani.
Ani, ya kuma ƙara da cewar, hukumar za ta tabbatar da ɗaukar ma’aikatan da su ka dace, duba da kyakykyawan tsarin tantance masu neman aiki a hukumar da ta samar.
“Akwai buƙatar masu neman aikin su halarci adireshin apply.policerecruitment.gov, domin tabbatar da halin da su ke ciki, bayan halartar screening, tare da sanin haƙiƙanin wuri, lokaci, da ranar da za su rubuta jarrabawoyinsu na CBT”” a cewarsa.
Ana kuma buƙatar masu rubuta Jarrabawar da su halarci cibiyoyin ɗauke da slip ɗin da su ka cire a shafin hukumar.