An Fara Zanga-Zangar NLC A Abuja Da Lagos
Wasu rahotanni da ke fitowa daga babban birnin tarayya Abuja, tare da birnin Lagos na bayyana yadda zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta shirya gudanarwa a ƙasar nan ta ɗauki harami.
Tuni dai masu zanga-zangar waɗanda su ka fara daga Computer Village, da ke yankin Ikejan jihar Lagos, su ka fantsama zuwa sassan jihar da dama.
A babban birnin tarayya Abuja ma dai, tuni masu zanga-zangar da ke ɗauke da Kwalaye masu rubutun nuna adawa da tsadar rayuwa su ka mamaye Harabar Majalissar Tarayya.
Fitowar masu zanga-zangar kuma, ya jawo cunkoson Ababen hawa, tare da tilastawa mutane da dama tafiyar ƙafa.
Idan mai bibiyar Rariya Online zai iya tunawa dai, a ya yin zaman da ƙungiyar ta NLC ta gudanar tun a ranar 8 ga watan Fabrairun da mu ke bankwana da shi ne, ta bawa Gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14, sakamakon gaza aiwatar da yarjejeniyoyin da su ka ƙulla a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, bayan janye tallafin manfetur.