Ƙasashen Ƙetare

An Fuskanci Girgizar Ƙasa A Kogin Banda, Na Indonesia

Wani bincike da Cibiyar ƙasa da yanayi ta Amurka ta gudanar, ya bayyana yadda girgizar ƙasa mai saurin 7.1, ta doshi tekun Banda na ƙasar Indonesia, da safiyar yau, sai dai zuwa yanzu babu rahoton asarar dukiya ko jikkata.

Ka zalika, zuwa yanzu babu gargaɗin yiwuwar samun igiyar ruwan ambaliya sakamakon girzizar ƙasar, duk kuwa da yadda saurin girgizar ya ƙaru zuwa 6.9 da misalin ƙarfe 11 da mintuna 53 na safiya agogogon Najeriya, kamar yadda cibiyar ta USGS ta bayyana.

Girgizar ƙasa dai, na faruwa sakamakon yunƙurin gyara zama da ƙasa ke yi, inda a mafi yawan lokuta hakan ke haifar da rushewar gine-gine.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button